

Karanta rubutu kawai domin rage cin dataAsalin hoton, APBayanan hoto, Majalisar dinkin duniya ta ayyana cutar Ebola a matsayin babban kalubale na tsaro da zaman lafiya19 Satumba 2014Kasar Saliyo ta sanya dokar hana fita na tsawon kwanaki uku a yunkurin da takeyi na kawo karshen yaduwar cutar Ebola.Dokar ta fara aiki ne a ranar Juma'a kuma za ta kare a ranar Lahadi mai zuwa, kuma a tsawon kwanakin jami'an sa kai za su bi gida-gida don gano masu dauke da cutar Ebola.Haka kuma za a yi amfani da wannan dama wajen wayar da kan daukacin 'yan kasar miliyan shida a kan cutar, tare da raba musu sabulai.Gwamnatin Saliyo ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai domin kawo karshen cutar ebola a kasar.
Lean: n/a · Source quality n/a · Factual vs opinion n/a.
© 2026 Vistoa. All rights reserved.
Limited excerpts, attribution, analysis, and outbound publisher links remain core product boundaries.